Rundunar haɗin gwiwa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya da ke yaƙi a Yemen ta faɗa ranar Lahadi cewa ta kama wani jirgi maras matuƙi maƙare da bama-bamai a Yemen da ƙungiyar Houthis ta aika zuwa Saudiyya.
Kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito cewa tuni aka lalata jirgin.
Wani kwamandan Houthis ya ce sun kai hare-hare kan filin jirgin sama na Abha a Saudiyya da jirage marasa matuƙa ranar Lahadi.
An kai hare-haren ne kan sansanin sojoji kuma an yi nasara, in ji mai magana yawun ƙungiyar Yahya Sarea.
Sai dai gamayyar rundunar Saudiyyar ba ta yi magana kan harin Abha ba.

0 σχόλια:
Post a Comment