Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayyana kaɗuwarsa da ambaliyar ruwan da ta faru a Jihar Kebbi da ke arewacin ƙasar yana mai cewa "ta kawo wa yunƙurimmu na bunƙasa noman shinkafa cikas".


Shugaban ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon Twitter da ya wallafa yau Lahadi fiye da mako guda bayan faruwar bala'in, wanda ya yi sanadiyyar lalata gonaki da dama tare da jawo asarar rayuka.


Ƙananan hukumomin da ambaliyar ta fi shafa su ne Suru Bunza da Kalgo da Birnin Kebbi.


"Ban ji daɗin ambaliyar ruwan da ta faru a Jihar Kebbi ba, wadda ta jawo rasa rayuka da kuma lalata gonaki," in ji Buhari.


Ya ci gaba cewa: "Wannan wani koma-baya ne ga yunƙurimmu na haɓaka noman shinkafa a cikin gida a matakan da muke ɗauka don hana shigowa da ta waje.


"Wannan labari maras daɗin ji ya zo a lokacin da manoman Najeriya ke cikin wani hali kuma suke ƙoƙarin girbar amfanin gona mai yawa a wannan shekara domin rage hauhawar farashin kayan abinci."


Social embed from twitter


0 σχόλια:

Post a Comment

 
Top