<iframe width="400" height="500" frameborder="0" src="https://www.bbc.com/hausa/media-53978463/embed"></iframe>
Kalli bidiyon yadda likitoci a Yola suka raba tagwaye da aka haifa da hanta ɗaya
Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Yola a jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya ta yi nasarar raba wasu tagwaye ta hanyar tiyata da aka haifa manne da juna.
Tawagar asibitin da ta kunshi ma'aikata 48 ne ta gudanar da aikin, watanni takwas bayan haifar tagwayen.
Wannan shi ne karo na uku da Asibitin ta FMC Yola ke tiyatar raba tagwaye da aka haifa manne da juna a cewar shugaban cibiyar Farfesa Auwal Abubakar.
0 σχόλια:
Post a Comment