Jama'a suna ta yi min magana a kan siyasa tun a lokacin da nake babban bankin Najeriya. Ban taba ra'ayin siyasa ba har yanzu. "Yanayin gidan da na fito shine, muna kallon kanmu a matsayin shugabannin talakawa kuma kun san siyasa bata dace da hakan ba," yace. "Abinda zan iya cewa shine, wannan ba ita bace manufata. Ina tunanin akwai hanyoyin bautawa kasa. "Na fara a matsayin malamin makaranta. Bayan shekaru biyu da na kammala digirina na biyu, sai na fada bangaren banki. Na kasance ma'aikacin banki kuma daga baya basarake."
Sanusi ya ce yana da burin wallafa litattafai uku yayin da yake jami'ar Oxford kuma daya daga ciki zai yi magana ne a kan shari'a. Daya kuwa zai mayar da hankali ne wurin magana a kan yadda babban bankin Najeriya ke daukar mataki a kan rikicin kudi.
Ya ce littafin na uku zai rubuta shi ne a kan yadda Musulmai ke fassara wasu dokoki da kuma al'adu, wanda hakan ke kawo rashin ci gaba a arewacin Najeriya. "Akwai yuwuwar in koma aikina na farko da ban kammala ba har yau. Zan iya zama farfesa a jami'o'i daban-daban. "Babban abinda nake da shi shine, ba kowacce jami'a bace take da mutum mai digirin digirgir, tsohon shugaban banki kuma basarake ba," yace. "Wannan takardun nawa za su iya samo maka kowacce irin jami'a a duniya, koda kuwa Harvard, Oxford, Cambridge da sauransu ne. "Bana iya ganin abinda zai faru a gaba, don haka zan rungumi rayuwa yadda take tahowa. Ba sauri nake yi ba. "A gaskiya ina ganin kaina a matsayin mai hidimtawa jama'a, amma bana tunanin ofishin siyasa ba zai durkusar da ni ba." yace.

0 σχόλια:
Post a Comment